Home Labaru Kasuwanci Tattalin Arziki: Bashin Biliyoyin Dalolin Kudin Da Ake Bin Najeriya Da Wasu...

Tattalin Arziki: Bashin Biliyoyin Dalolin Kudin Da Ake Bin Najeriya Da Wasu Kasashe 9 Ya Yi Yawa-Bankin Duniya

55
0

Bankin duniya ya ce Najeriya ta shiga cikin jeren kasashe 10 da bashi ya yiwa katutu a duniya.

Bankin a wata sanarwa kan yanayin basusuka da cigaba da ake samu, ya ce Najeriya ta kasance ta biyar a jerin kasashen da ake bin tarin bashi inda aka bayyana basusukan da ake bin ta ya kai $11.7bn.

Indiya ke kan gaba inda ake bin ta $22bn, sai Bangladesh $18.1bn, Akwai Pakistan ita ma da basusukan ta suka kai $16.4bn, sai Vietnam$14.1bn.

Sauran ƙasashen da ke cikin wannan jere 10, akwai Ethiopia mai $11.2bn, Kenya ta ciyo bashin $10.2bn, Tanzania $8.3bn, Ghana ta na da $5.6bn, sai kuma Uganda mai $4.4bn.

Sanarwa ta kuma kara da cewa kudaden da bankin duniya kadai ke bin Najeriya wanda ba a raba ba sun kai $8.656bn a ranar 30 ga watan Yuni, 2021.