Home Labaru Diflomasiya: Koriya Ta Arewa Ta Gargadi Amurka Da Koriya Ta Kudu Kan...

Diflomasiya: Koriya Ta Arewa Ta Gargadi Amurka Da Koriya Ta Kudu Kan Rawar-Daji

66
0

Koriya ta Arewa ta gargadi makwabciyarta Koriya ta Kudu da kuma Amurka, da cewa za su haddasa gagarumin tashin hankali na tsaro idan suka ci gaba da shirinsu na atisayen hadin-gwiwa na soji.

Wannan ita ce sanarwa ta biyu a cikin kwana biyu da gwamnatin Koriya ta Arewar ta fitar, wadda ke nuna gwamnatin na kara wannan barazana ne, kafin rawar-dajin kasashen biyu kawayen juna, abin da Koriya ta Arewar ke dauka a matsayin wani shiri na yaki.

Gwamnatin Koriya ta Arewa ta gargadi makwabciyar tata Koriya ta Kudu da cewa muddin ta sake ta shiga wannan atisayen soji da Amurka, hakan zai iya bata duk wata dama ta farfado da dangantakar kasashen biyu, wadanda a hukumance har yanzu suna yaki ne, duk da kawo karshen rikicinsu a 1953.

To sai dai kuma duk da wannan gargadi, na Pyongyang, Seoul da Washington din ko gezau, domin dubban sojojin Koriya ta Kudun da kuma dakarun Amurka sun ci gaba da shirye-shiryensu na wannan atisaye na shekara-shekara da za su yi a mako mai zuwa.