Home Labaru Kiwon Lafiya Tatsar Kudade: Akpabio Ya Ce ‘Yan Siyasa Sun Maida Hukumar Nddc Na’urar...

Tatsar Kudade: Akpabio Ya Ce ‘Yan Siyasa Sun Maida Hukumar Nddc Na’urar Atm Tsawon Shekara 19

586
0

Ministan kula da harkokin yankin Niger Delta Sanata Godswill Akpabio, ya ce hukumar NDDC da aka dorawa alhakin raya yankin ta zama na’urar ATM, da ‘yan siyasar yankin ke tatsar kudaden da suke kashewa wajen yakin neman zabe.

Ministan ya bayyana haka ne yayin karbar bakuncin tawagar kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN a nan Abuja.

Sanata Akpabio, ya ce matsalolin rashawa da almundahana sun dade da yiwa hukumar raya yankin na Niger Delta NDDC, katutu taswon shekara 19, kafin nada shi ministan lura da yankin a shekarar 2015.

Tsohon gwamnan na Akwa Ibom, ya ce kamata yayi majalisun dokoki su fadada binciken da suke kan laifukan sace kudaden hukumar ta NDDC na tsawon shekaru 19, a mai makon zarge zargen almundahanar kudaden daga watan Fabarairu zuwa Yuli na shekarar 2020.

Ministan, ya kara da cewar jumillar Naira tiriliyan 5 gwamnati ta ba hukumar ta NDDC a tsawon shekaru 19, ba tare da an aiwatar da ayyukan da aka tsara za a yi das u  ba.

Leave a Reply