Home Labaru Juyin Mulki: ECOWAS Da Sojin Mali Sun Cimma Matsaya

Juyin Mulki: ECOWAS Da Sojin Mali Sun Cimma Matsaya

441
0

Wakilan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, wato ECOWAS ko SEADIAO da rundunar sojin da ta yi juyin mulki a Mali sun amince da yarjejeniya kan batutuwa da dama, kwana guda bayan sun fara tattaunawa kan yadda kasar za ta koma kan turbar mulkin dimokradiyya.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda shi ne ke jagorantar sulhu tsakanin bangarorin biyu, ya ce an samu damar cimma matsaya kan batutuwa da dama ko da yake ba a cimma matsaya kan komai da komai ba tukuna.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa wakilan ECOWAS sun ce shugabannin sojin sun bayar da shawarar kafa gwamnatin rikon kwarya ta soji wacce za ta kwashe shekara uku tana duba ginshikan kasar ta Mali.

Sun ce sun kuma amince su saki shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta, da suka yi wa juyin mulki.

ECOWAS dai ta nanata kiran mayar da Mr Keïta, kan mulki, sai dai dubban ‘yan kasar ta Mali sun fantsama kan titunan babban birnin kasar, Bamako, inda suka rika nuna goyon bayan su ga juyin mulkin.

Leave a Reply