Home Labaru Kiwon Lafiya Tashin Hankali: Sabon Nau’in Cutar Korona Ya Gauraye Afirka Ta Kudu –...

Tashin Hankali: Sabon Nau’in Cutar Korona Ya Gauraye Afirka Ta Kudu – Ramaphosa

197
0

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da tsauraran matakan taƙaita yaɗuwar cutar korona, don shawo kan abin da ya kira ƙarin bazuwar annobar mai tayar da hankali da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Ya ce asibitocin gwamnati da masu zaman kansu tuni sun kusa cika, sannan ana fama da ƙarancin gadaje a sashen kula da masu matsananciyar jinya.

Mista Ramaphosa ya ce sabon nau’in ƙwayar cutar da ya fi saurin yaɗuwa, ga alama a yanzu ya bayyana a duk faɗin ƙasar.

Sabbin matakan sun ƙunshi dokar taƙaita fita da kuma sa takunkumi ala tilas a cikin jama’a.

An kuma hana sayar da barasa da kuma duk wani taro a cikin gida ko waje.

A ranar Lahadi, adadin mutanen da suka kamu da korona a Afirka ta Kudu ya haura miliyan ɗaya tun bayan ɓullarta a watan Maris.