Home Labaru Suka: Trump Ya Yi Wa Hukumomin Amurka Gagarumin Ta’adi- Joe Biden

Suka: Trump Ya Yi Wa Hukumomin Amurka Gagarumin Ta’adi- Joe Biden

305
0

Hukumomi masu matuƙar muimmanci ga tsaron Amurka suna cikin wani ‘mawuyacin hali’ a hannun gwamnatin Mista Trump inji zababben shugaba Joe Biden.

Mista Biden ya ce ya ce ba a ba shi bayanan da yake bukata, ciki har da bayanai daga ma’aikatar tsaro kan batutuwan tsaron ƙasa a wannan lokacin da yake shirin karban ragamar mulki.

Ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi da masu yi masa hidima kan tsaron cikin gida da harkoki da kasashen waje. Ranar 20 ga watan Janairu Mista Biden zai zama shugaban ƙasa amma Shugaba Trump ya ki amincewa da shan kayen da yayi a hannun Joe Biden

Leave a Reply