Home Labaru Hare-Haren Masu Ikirarin Jihadi Na Karuwa A Jamhuriyar Nijar – Amnesty

Hare-Haren Masu Ikirarin Jihadi Na Karuwa A Jamhuriyar Nijar – Amnesty

20
0

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International, ta ce cikin shekarar nan hare-haren da mayakan jihadi ke kai wa yammacin jamhuriyar Nijar, sun munana, ya yin da lamarin ya fi shafar kananan yara.


A cikin rahoton da kungiyar ta fitar, ta ce tashin hankalin da mayakan suka haddasa a yankin Tilaberi mai makoftaka da iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso, ya kazanta a dan tsakanin nan.
Amnesty ta kara da cewa wata kungiya mai alaka da al-Qa’eda na kara kaimi wajen horas da yara maza domin shiga cikinta.
An dai rufe daruruwan makarantu a yankin Tillaberi, sakamakon hare-haren da mayakan jihadi ke kai wa.
A karshe rahoton ya zargi jami’an tsaron jamhuriyar Nijar ba wai kawai da gaza kare rayukan farar hula kadai ba, har da cin zarafin da ake zargin suna aikatawa a yankunan da lamarin ya fi Kamari.