Home Labaru Taron Majalisar Dinkin Duniya: Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka

Taron Majalisar Dinkin Duniya: Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka

11
0

Fadar shugaban kasa, ta ce a ranar Lahadi ne shugaba Buhari ya kama hanyar zuwa kasar Amurka don halartar taron majalisar Dinkin Duniya karo na 76.

Fadar shugaban kasan ta ce Shugaba Buharin, ya tafi Amurka ne don halartar taron wanda zai gudana a birnin New York.

Mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adeshina yace shugaba Buhari zai yi jawabi a taron, a muhawarar da za a yi a ranar Juma’a 24 ga watan Satumba, inda zai yi magana kan maudu’in taron da sauran al’amuran da suka shafi duniya.

A cewar Adesina, tawagar shugaban na Najeriyar za ta halarci wasu muhimman taruka kamar na zagayowar cika shekara 20 da kulla yarejejeniyar Durban, wanda ya kunshi batutuwan da suka shafi biyan diyya da tabbatar da adalci da daidaito ga ‘yan asalin nahiyar Afirka.

A Wannan shekarar, taron zai mayar da hankali ne kan yadda kasashen duniya za su farfado daga bala’in annobar COVID-19, da sauyin yanayi da kuma kare hakkin bil adama.

Ana sa ran da yardan Allah shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya ne a ranar 26 ga watan Satumba.