Shugabannin kasashen kungiyar yankin Sahara sun gudanar da wani taron gaggawa a Chadi wanda ya mayar da hankali akan rikicin kasar Sudan .
Shugaban Chadi Idris Deby Itno, ya bayyana damuwa matuka da cewa yanayin da wasu kasashe ke dab da fadawa kan iya haifar da wani sabon rikici a kan iyakokin kasashen su.
Ya ce a kasar Sudan jam’iyyar NCP ta tsohon shugaban kasar Omar El Beshir , ta kalubalanci juyin mulki da sojojin kasar suka yi, ta kuma bukaci ganin an sako ilahirin shugabanin ta dake tsare yanzu haka.A karshe jam’iyyar a wata sanarwa da ta fitar na nuni cewa kwace mulki ta hanyar kifar da gwamnati ya sabawa kudin tsarin mulki wanda hakan ke da babban hadari.