Home Labaru Tarihi: Jirgin Isra’ila Ya Sauka Morocco A Karon Farko

Tarihi: Jirgin Isra’ila Ya Sauka Morocco A Karon Farko

257
0

Tawagar haɗin gwiwa tsakanin Isra’ila da Amurka ta isa Morocco cikin jirgin sama na farko da a tarihi ya tashi daga Isra’ila ya sauka Morocco.

Wannan lamari mai cike da tarihi ya tabbata ne bayan shiga tsakani da Amurka ta yi ta ƙulla yarjejeniyar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Tawagar da ta isa Moroccon za ta saka hannu kan wasu yarjejeniyoyi da suka haɗa da na jigila da wasu yarjejeniyoyi da za su taimaka wa ƙasashen biyu wajen ƙara danƙon zumunci.

A watannin da suka gabata, an samu sasanci matuƙa tsakanin wasu ƙasshen Larabawa da kuma Isra’ila. Sai dai Falasɗinawa ba su maraba da wannan sulhu sakamakon sun so a ce ba a yi wannan sulhun ba sai an sasanta tsakanin su da Isra’ila.

Leave a Reply