Home Labaru Laifi: An Ci Tarar Thuram Saboda Tofa Wa Abokin Sa Yawu A...

Laifi: An Ci Tarar Thuram Saboda Tofa Wa Abokin Sa Yawu A Fuska

284
0

Hukumar Kwallon Kafar Jamus ta haramta wa Marcus Thuram na Borussia Monchengladbach buga wasanni shida tare da cin sa tarar Euro dubu 40 saboda laifin da ya aikata na tofa wa abokin hamayyar sa yawu a fuska.

Hoton bidiyo ya nuna cewa, Thuram mai shekaru 23, ya tofa yawun ga dan wasan baya na Hoffenheim, Stefan Posch a wasan da Borussia ta sha kashi da ci 2-1.

A bangare guda kungiyar sa ta Borussia Monchengladbach ita ma za ta ci tarar sa daban har kudin da ya kai Euro dubu 150, wato kwatankwacin albashin sa na wata guda a kungiyar.

Kungiyar za ta zuba kudin tarar a asusun agazawa marasa karfi kamar yadda jaridar Bild ta rawaito.

Thuram dai, da ne ga tsohon dan wasan Faransa da ya lashe kofin duniya a shekarar 1998, wato Lilian Thuram, yayin da ya nemi afuwa kan laifin da ya aikata a shafin sa na Instagram.

Leave a Reply