Home Labaru Takaddama: Wadume Ya Ambaci Sunan Darius A Matsayin Mai Daukar Nauyin Sa

Takaddama: Wadume Ya Ambaci Sunan Darius A Matsayin Mai Daukar Nauyin Sa

14076
0

Kasurgumin mai garkuwa da mutane Hamisu Bala Wadume, ya bayyana sunan gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku a matsayin wanda ke daukar nauyin sa ya na tafka ta’asa kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Wadume ya bayyana haka ne, yayin da ake binciken sa a helkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, inda ya ce Gwamna Darius ne ya ba shi naira miliyan 6.

Haka kuma, Wadume ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa, Darius ya ba shi naira miliyan 2 a gidan sa da ke garin Ibbi, sannan ya kara ma shi naira miliyan 6 yayin da su ka hadu a Jalingo.

Yayin da wasu jama’ar jihar Taraba su ka bayyana bacin ran su game da hannun gwamnan a cikin irin wannan badakala, wasu kuma na ganin ba lallai ne a ce Darius ya san abin da Wadume ya ke yi ba, sai dai tuni gwamnan ya musanta wannan zargi.