A yayin zaman shari’ar alkalin kotun da aka gabatar da tsohon shugaban na Sudan, Omar al-Bashir, ya sheda masa cewa an samu tarin kudaden waje da na kasar da yawansu ya kai dala miliyan takwas a gidansa.
Karanta wannan: Take Hakki: An Fara Shari’ar Omar Al-Bashir Na Sudan
Mai shari’ar ya tuhumi dadadden shugaban na Sudan mai shekara 75 da mallaka da kuma amfani da kudin ta haramtacciyar hanya, abin da shi kuma ya musanta.
A lokacin da alkalin yake masa tambayoyi a karon farko, a karo na uku da yake bayyana a kotu, al-Bashir ya ce Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman ne ya turo masa kudin dala miliyan 25.
Ya ce ba wai ya yi ko yana amfani da kudin ba ne don amfanin kansa, ya ce ajiye kudin da ya yi a gidansa karramawa ce ga Yariman na Saudiyya domin shi ya bukaci hakan:
Ya ce ba a kai kudin Babban Bankin Sudan ba, saboda suna son sirrin ta, inda kudin suka fito ne, kuma sun yi hakan ne domin abinda, Yariman ya bukaci a yi ke nan.
Ya kara da cewa zai so
a ce wannan kotu ce dake zamanta a sirri, domin kada a bayyana sunan Yariman.
Saboda ba ya son sunansa ya bayyana a ko ina.
You must log in to post a comment.