Tsohon ɗanwasan Manchester United da Faransa Raphael Varane ya yi ritaya daga taka leda yana ɗan shekara 31.
Varane ya koma tamaula a ƙungiyar Como ne a watan Yuli a kyauta, amma ya ji rauni a was an sa na farko da suka fafata da Sampdoria a watan Agusta.
Sai dai ɗan wasan bayan, ya ce zai cigaba da kasancewa a ƙungiyar a wani matsayin daban ba na taka leda ba.
Varane ya fara taka leda ne a ƙungiyar Lens ta Faransa, inda ya yi kaka ɗaya kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2011.
Ya yi shekara 10 a ƙungiyar ta Spain, inda ya lashe kofi 18, ciki har da La Liga 3 da Champions Leagues huɗu.