Home Labaru Ta’ammuli Da Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Kama Mutane 140 A Jihar Kano

Ta’ammuli Da Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Kama Mutane 140 A Jihar Kano

209
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen jihar Kano, ta ce a watan Agusta ta kama mutane 140 da ta ke zargi da ta’ammuli da miyagun kwayoyi a a fadin jihar.

Shugaban hukumar, Ibrahim Abdul, ya ce jami’an sa sun kama mutanen ne a samamen da su ka kai a tsakiyar birnin Kano da kuma wasu kananan hukumomi.

Ya ce, a tsakanin lokacin hukumar ta kwace miyagun kwayoyi masu nauyin kilogram 501.98 wanda hakan ke nuna samun sauki a yawan shan miyagun kwayoyin da fasa-kwabrin su da ake yi a jihar.