Home Labaru Ta’Addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matar Kansila Da Jaririn...

Ta’Addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matar Kansila Da Jaririn Ta A Zamfara

78
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta ce wasu ‘yan bindiga sun sace matar wani tsohon kansila Babangida Ibrahim da jaririn ta ɗan watanni 7.

Da ya ke tabbatar da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu, ya ce maharan sun kai hari gidan tsohon kansilan da ke Damba a yankin Gusau  da misalin karfe 12:00 na dare a ranar Larabar nan.

SP Muhammad Shehu, ya ce tsohon kansilan ya tsira da harbin bindiga a jikin sa, kuma a halin yanzu ana ba shi kulawa a asibiti.

Ya ce Jami’an yan sanda na ci-gaba da gudanar da bincike da kuma bibiyar ‘yan bindigar domin kuɓutar da mutanen cikin koshin lafiya.