Home Labaru Zargin Almundahana: EFCC Ta Gayyaci Tsohon Gwamnan Bayelsa Seriake Dickson

Zargin Almundahana: EFCC Ta Gayyaci Tsohon Gwamnan Bayelsa Seriake Dickson

93
0

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar Bayelsa ta Yamma Henry Dickson, ya musanta zargin wawure baitul malin jihar yayin da ya ke kan kujerar gwamnan jihar.

Wata kungiya mai zaman kan ta ce ta shigar da kara, bisa zargin tsohon gwamnan da yin sama da fadi da kudaden gwamnati a cikin shekaru 8 da ya yi a matsayin gwamnan jihar.

Dickson ya gabatar da kan shi a ofishin hukumar, bayan ya samu takardar gayyatar da aka aika ma shi bisa zargin barnata kudaden gwamnati da cin amanar aiki a tsawon shekaru 8 da yayi a matsayin gwamna.

Yayin zantawa da manema labarai, Dickson ya ce ya bayyana kadarorin sa kamar yadda doka ta tanada a lokuta da dama a ofishin hukumar kula da da’ar ma’aikata kafin ya tsaya takarar gwamna.

Ya ce duk kaddarorin ya mallake su ne ta hanyar rancen da ya biya a hankali da kudaden albashin sa, kuma ciki akwai guda da bai karasa biya ba kuma ya gabatar wa hukumar EFCC takardun.