Rahotanni na cewa, masu garkuwa da mutane sun sake bayyana a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda su ka yi awon gaba da fasinjoji da dama.
Wani shaidun gani da ido da ya tsallake rijiya da baya Mohammed Dambatta, ya ce masu garkuwa da mutanen sun tare hanyar ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Litinin da ta gabata a Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia.
Dambatta, ya ce masu satar mutanen sun bude wutar kan mai uwa da wabi ne, lamarin ya tilasta wa motoci akalla 15 tsayawa, inda su ka yi awon gaba da fasinjoji da dama.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata, jami’an ‘yan sanda sun ce sun yi nasarar kama wani Abubakar Ibrahim da ake zargi da kashe marigayi Sarkin Adara Maiwada Galadima na Karamar Hukumar Kajuru.
Matsalar garkuwa da mutane dai na ci gaba da addabar sassa da dama na Nijeriya, musamman jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da kuma Sokoto.
You must log in to post a comment.