Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mata da dama masu zaman kan su, a wani mataki na tsabtace jihar kafin Azumin Ramadan na wannan shekarar.
Wata majiya ta ce hukumar ta kai samame ne a gidajen da ake tara mata masu zaman kan su a birnin Kano da wasu kananan hukumomi.
Babban daraktan hukumar ta Hisba a Kano Mallam Abba Sufi, ya ce sun kama Mata masu zaman kan su guda 26 a garin Kano kawai, kuma tuni an gurfanar da wasu daga cikin su a gaban kotu.
Ya ce Kotu ta yanke wa wasu hukuncin daurin shekara daya a karkashin dokar hana karuwanci.
Abba Sufi, ya ce sun kai samame a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Tamburawa da su ka yi suna wajen tara mata masu zaman kan su.
You must log in to post a comment.