Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Jihar Katsina

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Jihar Katsina

1323
0

Yayin da ake ci-gaba da fuskantar kalubale na nau’ukan ta’addanci daban-daban ba dare ba rana, musamman a Arewacin Nijeriya, yanzu haka rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun sake kai wani mummunan hari a jihar Katsina.

Harin da ya auku da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata a kauyen Zakka na karamar hukumar Safana, ya salwantar da rayukan ‘yan’uwan juna uku da su ka fito ciki daya kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

An dai gabatar da gawarwakin wadanda aka kashe a fadar sarkin Katsina Mai Martaba Abdulmumin Kabir, bayan an garzaya da su da yammacin Asabar tare da Mahaifiyar su cikin zubar hawaye.

Kakakin masarautar Katsina Mallam Iro Bindawa, ya shawarci dagacin kauyen Zakka ya bayyana wa fadar Katsina a rubuce duk yadda ta kasance yayin aukuwar wannan mummunan lamari.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce harin ya auku ne yayin da ‘yan ta’adda su ka kai farmaki a kan mutanen a wata gonar su da ke bayan gari.