Home Labaru Wata Sabuwa: Majalisar Kaduna Ta Amince Da Dokar Tantance Masu Wa’azi

Wata Sabuwa: Majalisar Kaduna Ta Amince Da Dokar Tantance Masu Wa’azi

385
0

Majalisar dokoki ta jihar Kaduna, ta amince da wata sabuwar dokar sa ido a kan malamai masu wa’azi daga bangaren Musulmi da Kirista.

Aikin dokar dai shi ne, tattance malaman da ya kamata su rika yin wa’azi, tare da ba su lasisi a matsayin shaidar amincewar gwamnati.

Haka kuma a karkashin dokar, duk wanda aka samu da laifin kunna wa’azi ko gabatar da shi ta hanyar amfani da na’urar amsa kuwwa a masallaci ko mujami’a daga misalin karfe 11 na dare zuwa 4 na asuba, zai fuskanci hukuncin biyan tarar da ba za ta gaza naira dubu 200 ba, ko kuma daurin akalla shekaru 2 ko ma sama da haka.

Dokar, wadda makasudin ta shi ne tabbatar da hadin kan mabiya addinai daban-daban a jihar Kaduna, a baya ta fuskanci suka daga wasu malaman addinai, a lokacin da aka gabatar da kudurin ta a zauren majalisar dokoki ta jihar ta Kaduna a shekara ta 2016.

Leave a Reply