Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Karamar Hukuma A Kebbi

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Karamar Hukuma A Kebbi

1142
0

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan binduga ne, sun harbe matar shugaban karamar hukumar Bunza, da wani jami’in dan sanda da kuma dan kungiyar sintiri ta sa-kai a garin Zogirma a jihar Kebbi.

Lamarin dai ya faru ne, bayan ‘yan bindigar sun gaza samun damar sace matar shugaban karamar hukumar.

Yanzu haka wasu mutane uku da ‘yan bindigar su ka harba su na sashen bada kulawar gaggawa a asibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi.

Wani mazaunin garin Zogirma Aliyu Usman ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun yi harbi domin firgita jama’a bayan sun isa garin, kafin daga bisani su yi awon gaba da matar daga gidan ta.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Bello Zogirma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya na mai cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin ne da misalin karfe 1da minti 40 na safiyar Lahadin da ta gabata.

Leave a Reply