Kungiyar masana magunguna ta kasa PCN, ta rufe manya da kananan shagunan saida magunguna 231 a jihar Nasarawa.
Shugaban kungiyar Stephen Esumobi ya sanar da haka a garin Lafia, inda ya ce kungiyar ta yi haka ne sakamakon binciken da ta gudanar a kan shagunan da ke saida magunguna a jihar.
Matsalolin da su ka sa kungiyar ta rufe shugunan kuwa sun hada da rashin tsaftace muhalli, da rashin lasisi, da rashin sabunta takardun da wa’adin su ya kare, da saida jabun magunguna da rashin kwararren masanin magani a shagunan.
Esumobi, ya ce shagunan da su ka rufe sun hada da manyan shagunan saida magunguna 18 da kananan shaguna 213.