Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sun Sace Ɗalibai A Kwalejin Noma...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sun Sace Ɗalibai A Kwalejin Noma Dake Zamfara

176
0

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai da malamai a Kwalejin Noma da Kula da lafiyar dabbobi da ke garin Bakura a jihar Zamfara.

Mataimakin rijistaran kwalejin Malam Aliyu Bakura, ya tabbatar da labarain yayin zantawarsa da kafar yada labarai ta BBC.

Ya ce sun kashe mutum huɗu da suka haɗa da ɗan sanda ɗaya da masu gadi uku.

Ya ce “a ranar Lahadin da ta gabata ne da misalin  ƙarfe 10 na dare suka shiga makarantar inda suka rika harbe-harbe kafin daga bisani suka kwashe ɗalibai 15 da kuma wani malami da matarsa da ƴaƴansa biyu..

Malam Aliyu ya ce maharan suna da matuƙar yawa kuma sun haura katanga ne sannan sun fi sa’o’I biyu a cikin makarantar suna harbe-harbe.

Ko a watan Yuli ƴan bindiga sun taɓa shiga makarantar ɓangaren gidajen malamai suka sace shugaban Kwalejin ta Bakura.

Wannan na zuwa bayan ƴan bindiga suka kashe mutum sama da 40 a yankin mulkin Maradun da ke maƙwabtaka da Bakura.

Haka ma ƙaramar hukumar Talatar Mafara da ke maƙwabtaka da Bakura ƴan bindiga sun taɓa shiga makarantar sakandaren mata dake garin Jangebe inda suka sace ɗalibai.