Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wata Kotu Da Ke Hukumar Barikin...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wata Kotu Da Ke Hukumar Barikin Ladi

136
0

Wasu ‘yan bindiga biyar dauke da makamai sun kai hari wata kotu da ke karamar hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato, inda su ka yi awon gaba da mutane hudu da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya, ya ce mutanen da aka kubutar sun hada da Umar Adamu da Bashir Mohammed da Musa Usman da kuma Abdul Haruna, wadanda aka shirya za su gurfana a gaban alkali Nanpon Dadi.

Mai gabatar da kara a kotun, ce da misalin karfe 9 da rabi na safe ‘yan bindigar su ka kutsa kai harabar kotun su na harbi a sama, lamarin da ya ba su nasara a kan jami’an gidan yari da ke rakiyar wadanda ake zargi.

Yunkurin jami’an gidan yarin na neman dauki daga ‘yan Sandan da ke Barikin Ladi ya ci tura, inda ‘yan bindigar su ka tsere da wadanda ake zargin.

Daraktan gabatar da kara na Jihar Filato Jacob Longden ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an shaida wa rundunar samar da tsaro, kuma yanzu haka ta na bin sawun ‘yan bindigar.