Home Labaru Tsaro Ta’Addanci: Gwamna Masari Ya Bukaci Katsinawa Su Nemi Makaman Kare Kawunan Su

Ta’Addanci: Gwamna Masari Ya Bukaci Katsinawa Su Nemi Makaman Kare Kawunan Su

40
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bukaci mutane musamman wadanda ke zaune a wuraren da ke da karancin tsaro su nemi makamai domin kare kawunan su daga hare-haren ‘yan bindiga.

Masar ya bayyana haka ne a garin Jibia, yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya da jajenta wa ga al’ummar da hatsarin motar jami’an kwastan ya rutsa da su a makon da ya gabaya.