Home Labaru Ta’addanci: Gwamna Masari Ya Bukaci Da A Bude Wa ’Yan Bindiga Wuta...

Ta’addanci: Gwamna Masari Ya Bukaci Da A Bude Wa ’Yan Bindiga Wuta Ko Sun Shiga Cikin Mutane

10
0
Gwamnan Katsina Aminu Masari ya bukaci sojoji da su tsananta yaki da bata-garin ba tare da tsoron ko harin zai iya ritsawa da mutanen da babu ruwansu ba.

Gwamnan Katsina Aminu Masari ya bukaci sojoji da su tsananta yaki da bata-garin ba tare da tsoron ko harin zai iya ritsawa da mutanen da babu ruwansu ba.

Masari ya ce matakan da sojoji suka dauka a kan ’yan bindiga sun takura miyagun ta yadda suke kokarin shigowa cikin al’ummomi, amma duk da haka kada sojoji su raga musu.

Sai dai kuma ya shawarci sojojin da su dauki matakan takaita yiwuwar kashe mutanen da babu ruwansu a irin hakan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ziyarce shi domin sanin hakikanin nasarar da ake samu a yaki da ’yan bindiga.

A nasa bangaren, Lai Mohamme ya ce, “Sulhu da ’yan bindiga abu ne da gwamnati mai ci ba za ta lamunta ba.”

Shi ma da yake nasa jawabi, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, ya ce kuskure ne a yi sulhu da irin wadannan mutane.