Home Labaru Dakile Ta’addanci: Gwamnatin Jihar Kano Ta Haramta Nuna Fina-Finan Garkuwa Da Mutane

Dakile Ta’addanci: Gwamnatin Jihar Kano Ta Haramta Nuna Fina-Finan Garkuwa Da Mutane

87
0
Gwamnatin Kano ta haramta nunawa ko sayar da fina-finai da ke tallata garkuwa mutane ko kwacen waya ko ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.

Gwamnatin Kano ta haramta nunawa ko sayar da fina-finai da ke tallata garkuwa mutane ko kwacen waya ko ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.

Sabuwar dokar wani yunkuri ne na gwamnatin jihar domin magance matsalolin uku da ke ci wa Jihar Kano tuwo a kwarya, duk da kokarin da hukumomin tsaro ke yi domin shawo kansu.

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar cewa “Daga yanzu an haramta fina-finai da ke nuna garkuwa da mutane ko ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kwacen waya, matsalolin da ke illata al’ummar Jihar Kano.”

Shugaban hukumar, Isma’il  Naabba Afakallah, ya ce manufar haramta nau’ikan fina-finan ita ce kawar da yiwuwar matasan Kano su koyi aikata miyagun laifuka a dalilin kallon fim.

Ba kowane matashi ne ke da hankalin fahimtar sakon da ke cikin kirkirarrun fina-finan ba; Wani zai iya dauka da gaske ne, ya je ya aikata irin abin da ya gani a ciki; Saboda haka ya zama wajibi mu dauki mataki tun ba mu makara ba”, inji Afakallah.