Home Labaru Ta’addanci: Firaministan Libya Ya Sha Da Ƙyar Bayan Harin ‘Yan Bindiga

Ta’addanci: Firaministan Libya Ya Sha Da Ƙyar Bayan Harin ‘Yan Bindiga

191
0

Firaministan Libya Abdulhamid al-Dbeibah ya tsallake rijiya da baya a yunkurin hallaka shi da wasu ‘yan bindiga suka yi.

An yi wa motarsa ɓarin harsasai a lokacin da yake tafiya a birnin Tripoli da safiyar yau Alhamis, amma ba a yi nasarar kama su ba.

Ana ta samun tashin hankali tsakanin kungiyoyin da ba sa jituwa da juna a Libya kan wanda ya dace ya jagoranci kasar.

Nan gaba a yau ne ‘yan majalisa a gabashin ƙasar za su kaɗa ƙuri’ar wanda zai maye gurbin Mista al-Dbeibah, kodayake ya ce ba zai amince da sakamakon kuri’ar ba.