Home Home Ta’addanci: Dan Bindiga Ya Harbe Mutum 10 a Cikin Kanti a Amurka

Ta’addanci: Dan Bindiga Ya Harbe Mutum 10 a Cikin Kanti a Amurka

31
0

Wani dan bindiga ya kashe mutum aƙalla 10 a kantin Walmart da ke Chesapeake na Jihar Virginia ta Amurka.

Ana zaton manajan shagon ne ya harbe mutanen kafin daga baya ya harbi kan sa, kuma ya mutu daga bisani.

Hukumomin birnin na Chesapeake sun wallafa a shafin Twitter cewa ‘yan sanda sun tabbatar da wani mutum na harbe-harbe a Walmert inda aka samu rasa rayuka.

Har yanzu babu cikakken bayani amma wani ɗan sanda ya ce akwai mutum aƙalla 10 da aka kashe tared a raunata wasu da dama.

Ba a san dalilin da ya sa ya harbe mutanen ba zuwa yanzu.

‘Yan sanda suka ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:12 na dare agogon yankin, 4:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.