Kasashen yammacin Afrika sun yi wata ganawa da takwarorin su na Turai a Ghana a wani yunkuri na sake karfafa kawancen da ke tsakanin su a kokarin dakile barazanar hare-haren ta’addanci a yankunan da ba su saba ganin makamantan hare-haren ba.
Duk da ya ke babu wata sabuwar sanarwar hadaka game da matakan da taron na jiya ya dauka, amma dukkanin banagorin sun amince da tsaurara matakai don dakile barazanar ayyukan mayaka masu ikirarin jihadi a kasashen da ke yankin tekun Guinea.
Kasashen na yankin Tekun Guinea da suka kunshi Ghana da Benin da Togo da kuma Ivory Coast na ganin karuwar barazanar hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi wadanda ke tsallako iyaka ta arewaci daga kasashen Nijar da Burkina Faso.
Taron na birnin Accra na zuwa a dai dai lokacin da kasashen na yankin Tekun Guinea ke ci gaba da janye dakarunsu da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali bayan da kasar ta karfafa alakar tsaronta da Rasha.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce karuwar matsalar tsaro a yankin Sahel shi ke kokarin jefa ilahirin yankin yammacin Afrika a matsalar ta tsaro da hare-haren ta’addanci.
Shugabannin kasashe daga ilahirin kasashen na yankin Tekun Guinea da takwarorin su na Burkina Faso da Nijar ne suka halarci taron na jiya a Ghana baya ga wakilcin ECOWAS da kuma wakilan kasashen Birtaniya da Faransa da kuma kungiyar Tarayyar Turai.