Majiyar kamfanin dillancin labaran kasar Faransa (AFP) ya ruwaito cewa wasu maharan da ake kyautata zaton Boko Haram ne sun kashe mutum uku (masu saran itace) tare da awon gaba da kimanin mutum 40 a kauyen Wulgo da ke kusa da kan iyakar Kamaru a jihar Borno.
sun bayyana cewa maharan sun farmaki mutanen a lokacin da suke aikin faskaren itace a kauyen wanda yake kan iyakar.
Bugu da kari, wannan yanki ne wanda ya yi kaurin suna a ayyukan yan kungiyar wajen kai hare-haren sari-ka-noke.
Majiyar ta bayyana cewa mutanen sun gamu da ajalinsu ne a dajin Wulgo, a sa’ilin da suka je saran iatacn, inda har yamma ta yi babu labarinsu, wanda hakan ya jawo jami’an tsaron sa-kan su ka niki gari zuwa surkukin dajin, yayin da su ka tarar da gawawakin mutanen an harbe su har lahira.
“Mun samu gawawakin su kuma akwai alamar an kashe su ne a lokacin da su ke kokarin gudo wa, saboda dukan su an harbe su ne a baya,” in ji shugaban yan-sintirin yankin.
You must log in to post a comment.