Home Labaru Ta’addanci: An Kashe Mutum 3, Anyi Garkuwa Da 20 A Jihar Zamfara

Ta’addanci: An Kashe Mutum 3, Anyi Garkuwa Da 20 A Jihar Zamfara

312
0

Rahotanni na cewa an kashe mutane uku, yayin da aka yi garkuwa da kimanin mutane 20, biyo bayan sabon harin da aka kai karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Mutane da dama sun jikkata, sannan an yi fashin dabbobi akalla 500 a harin da ya gudana a mahaifar Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle.

Shugaban kasaramar hukumar Ahmed Abubakar, ya ce ‘yan fasin sun kai mamaya a kauyen Faru ranar Litinin da ta gabata, da kuma kauyen Bachiri a ranar Asabar, yayinda aka kai wani harin a kauyen Gama Giwa a ranar Lahadin da ta gabata..

Ahmed Abubakar, ya koka da yadda ake yawan kai hare-haren ta’addanci a garuruwan su, sannan sojoji ba za su iya shawo kan miyagun mutanen ba.

Ya ce su na samun hare-hare da dama a kowane mako, mutane su na mutuwa, sannan ana garkuwa da wasu saboda hukumomin tsaro ba su da kayayyakin aikin yakar ‘yan ta’addan.

Leave a Reply