Home Labaru Sulhu: Sanata Gobir Ya Ce Tattaunawa Da ‘Yan Da ‘Yan Ta’adda Ba...

Sulhu: Sanata Gobir Ya Ce Tattaunawa Da ‘Yan Da ‘Yan Ta’adda Ba Masalaha Bane

135
0

Shugaban Kwamitin Harkokin Tsaro da Tattara Bayanan Sirri na Kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya bayyana cewar sasantawa da ‘yan ta’adda da Gwamnati ke yi ba mafita ba ce ga samar da ingantaccen tsaro ga al’ummar kasar nan.

Sanatan ya bayyana cewar ko kadan babu dalilin da zai sa kowace irin Gwamnati ta zabi sasantawa da ‘yan ta’adda a matsayin mafitar kawo karshen ta’addanci a kasar nan.

Ya ce bai yarda da sasanci da ‘yan ta’adda ba. Babu bukatar a rika sasantawa da tsagerun da ke kisan jama’a da tayar da hankalin al’umma suna hana masu kwanciyar hankali.

Gobir ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke Sakkwato a jiya yana cewar mafita kawai ita ce gwabzawa da mayakan a fagen daga tare da ganin bayan su.

“A kan wannan ya kamata Gwamnati ta ci-gaba da yakar ‘yan ta’adda har zuwa karshe. Sun yi wa al’umma mummunar illa, sun sanya fargaba da tsoro a zukatan jama’a a wuraren da lamarin ya shafa.”