Home Home Su Obasanjo Suka Jefa Najeriya Cikin Tasku —Akinyemi

Su Obasanjo Suka Jefa Najeriya Cikin Tasku —Akinyemi

37
0
Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Farfesa Bolaji Akinyemi, ya soki tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a kan kiran da yi cewa ‘yan Nijeriya su zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa.

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Farfesa Bolaji Akinyemi, ya soki tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a kan kiran da yi cewa ‘yan Nijeriya su zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa.

Farfesa Akinyemi, ya ce Obasanjo ya na daga cikin wadanda su ka jefa Nijeriya cikin mawuyacin halin da take ciki a yanzu, don haka ba ya da bakin magana ballantana ya ce wa ‘yan Nijeriya ga wanda za su zaba.

Ya ce ba zai yiwu Obasanjo ya jefa jama’a cikin matsala sannan ya dawo ya na nuna masu cewa shi ya san maganin matsalolin Nijeriya.

Akinyemi ya yi wa Obasanjo wankin babban bargo ne, sa’o’i kadan bayan ya shawarci ‘yan Nijeriya su zabi Peter Obi a cikin sakon sa na taya su murnar shiga Sabuwar Shekara.