Home Home Taraba: Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutum Biyar Sun Kuma Kona Rugage...

Taraba: Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutum Biyar Sun Kuma Kona Rugage Da Dama

37
0
‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane biyar, tare da kona sama da rugage goma sha daya a kauyen Ngura da ke karamar hukamar Yorroo ta jihar Taraba.

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane biyar, tare da kona sama da rugage goma sha daya a kauyen Ngura da ke karamar hukamar Yorroo ta jihar Taraba.

Ardon Ngura Ummar Bello ya bayyana wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun je ne da manya makamai su ka fara kashe-kashe da kone-kone su ka kona gidaje akalla 15 baya ga mutane 5 da su ka hallaka da kuma kona kayan anfanin gona.

Ummar Bello ya ce suna cikin tashin hankali, na rashi samun gawar mahaifin sa Hassan Abdullah domin a yi ma shi jana’iza.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya faru a idon su Alhaji Abdu, ya ce suna cikin mawuyacin halin da ba su taba ganin irin sa ba, domin sun yi kokarin sanar da hukumomi amma har yanzu babu wani labara.