Home Labaru Soke Taro: Shugabannin Kudu-Maso-Kudu Sun Nemi Buhari Ya Ba Su Hakuri

Soke Taro: Shugabannin Kudu-Maso-Kudu Sun Nemi Buhari Ya Ba Su Hakuri

156
0

Shugabannin yankin Kudu-maso-kudu, sun bukaci Fadar Shugaban Kasa ta ba su hakuri a rubuce, dangane da taron da ta shirya yi da shugabannin amma daga baya ta soke.

Fadar Shugaban Kasa dai ta soke taron ne ba tare da bada wani dalili ba, bayan gwamnonin jihohin da sauran shugabannin yankin sun kammala shirya taron a Fatakwal.

Gwamnan Jihar Delta kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu-maso-kudu, ya ce fadar ta ce ta soke taron ne saboda wani taron gaugawa a kan matsalar tsaro da aka yi.

Soke taron dai ya bakanta wa shugabannin yankin rai matuka, inda su ka fassara lamarin da muzantawa da cin fuska da kuma cin zarafi, don haka su ka ce daukacin al’ummar yankin Kudu-maso-kudu su na so Fadar Shugaban Kasa ta nemi afuwa daga yankin.

Sun ce abin da aka yi wa yankin wulakanci ne da kuma nuna gwamnatin tarayya da Fadar Shugaban Kasa ba su dauki yankin Kudu-maso-kudancin Nijeriya da muhimmanci ba.