Home Labaru Raddi: Wike Ya Ce Neman Kujerar Shugaban Kasa Ya Sa Umahi Komawa...

Raddi: Wike Ya Ce Neman Kujerar Shugaban Kasa Ya Sa Umahi Komawa APC

204
0

Gwamnan jihar Rivers Nysom Wike, ya ikirarin gwamnan jihar Ebonyi Umahi cewa ya sauya sheka ne saboda jam’iyyar PDP ta ci amanar Inyamirai ba gaskiya ba ne.

Wike, ya ce kada Umahi ya kuskura ya fake da haka, ya na mai cewa shi dai shugabancin Nijeriya kawai ya ke so jam’iyyar APC ta ba shi takara.

Gwamnan Ebonyi David Umahi dai ya sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya ce nuna wariya da Kyama da rashin yi wa ‘yan kabilar Igbo adalci a jam’iyyar ne ya sa ya koma APC.

Ya kuma maida martani da cewa, bai taba neman kujerar shugaban kasa ba, kuma idan ma haka ai wakilai ne za su yi zabe ba shi zai zabi kan shi ba.

Umahi, ya kuma karyata masu cewa an yi ma shi alkawarin wata kujera ne a jam’iyyar APC, ya na mai cewa shi dai ya fi gani watakila APC ta fi yi wa Inyamirai adalci nan gaba fiye da PDP da yankin ta yi ta bauta mata sama da shekaru 20.