Rundunar Soji ta Operation Whirl Stroke, ta ce ta kama wani dilallin bindigogi Ardo Manu Abdulrahaman Maranewo, wanda jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo a Jihar Taraba.
Daraktan Sashen yada Labarai na Sojoji Manjo Janar Benard Onyeuko ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce Ardo Manu ya kware wajen sayarwa da kuma bada hayar bindiga ga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Ya ce dakarun soji sun kai samame maboyar ‘yan ta’adda da ke Maraba a karamar hukumar Ukum ta Jihar Benue.
Onyeuko, ya kuma bayyana yadda sojojin su ka kama wani dan bindiga mai shekaru 65 mai suna Ichen Igbaka da matar sa Salomi Gbaka.














































