Home Labarai Sojoji Sun Cafke Wadanda Suka Kai Hari Cocin Owo

Sojoji Sun Cafke Wadanda Suka Kai Hari Cocin Owo

472
0

Hedikwatar Tsaro ta Kasa ta ce, ta yi nasarar kama maharan da su ka kai hari a cocin Katolika da ke garin Owo na Jihar Ondo.

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Manjo-Janar Lucky Irabor ya bayyana haka, yayin wani taron tattaunawa da shugabannin kafafen yada labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja.

Manjo-Janar Irabor, ya ce sojoji sun kama ababen zargin ne tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro.

A ranar Lahadi 5 ga watan Yuni ne wasu ‘yan bindiga su ka afka wa cocin, inda su ka bude wuta a kan masu ibada su ka kashe mutane 40 tare d jikkata wasu da dama.

Leave a Reply