Home Labarai Nan Da ‘Yan Makonni Za a Magance Matsalar Tsaro A Yankinmu –...

Nan Da ‘Yan Makonni Za a Magance Matsalar Tsaro A Yankinmu – Wase

363
0

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Ahmed Idris Wase, ya tabbatar wa al’ummar mazabar sa cewa nan da makonni kadan za a kawo karshen kalubalen tsaron da su ke fuskanta.

Ahmed Idris Wase ya bada tabbacin ne, lokacin da ya ziyarci Sarkin Wase Muhammad Sambo Haruna a fadar sa domin jajenta ma shi bisa harin baya-bayan nan da aka kai a yankin.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Umar Muhammad Puma ya fitar, Wase ya ce nan ba da dadewa ba za a kawo karshen hare-haren da ‘yan bindiga ke kai ma wasu al’ummomi a yankin sa.

Ahmed Idris Wase ya shaida wa basaraken da al’ummar mazabar cewa, Gwamnatin Tarayya ta na daukar tsauraran matakai domin dakile matsalolin tsaro.

Ya ce ba a tattauna batutuwan tsaro da dabarun su a bainar jama’a, amma ya bada tabbacin nan da makonni kadan za a kawo karshen kalubalen tsaro a yankin.

Leave a Reply