Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwace wasu muhimman wurare a babban birnin ƙasar da kewaye, kwana guda bayan ta kai sabon farmaki kan dakarun RSF.
Sojojin sun bayyana nasarar da suka samu a Khartoum da kuma birnin Bahri, inda suka yi amfani da atilari da hare-hare ta sama da kasa.
A ranar Alhamis shugaban rundunar RSF Janar Hamdan Dagalo ya shaidawa taron MDD cewar ya shirya domin amincewa da tsagaita wuta.
To amma janar Abdel Fattah Al-Burhan ba zai yiwu a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba har sai RSF sun janye daga yankunan da suka mamaye tun farkon fara yakin basasar.














































