Home Labaru Sojin Nijeriya Sun Ce Sun Kashe Ɓarayin Daji 128 Da ‘Yan Boko...

Sojin Nijeriya Sun Ce Sun Kashe Ɓarayin Daji 128 Da ‘Yan Boko Haram 140

11
0

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce ta yi nasarar kashe ‘yan bindiga masu kai hare hare-hare da satar mutane 128 a yankin arewa maso yamma, da kuma da ‘yan Boko Haram 140 a arewa maso gabashin Nijeriya.

Mai magana da yawun Rundunar sojin Bernard Onyeuko ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana irin nasarorin da ayyukan rundunonin sojin su ka samu a sassan Nijeriya da ke fama da matsalolin tsaro.

Rundunar ta kara da cewa, alƙalumman sun shafi ayyukan rundunonin ta na tsawon makonni biyu, daga ranar 11 zuwa 25 ga Nuwamba, ta na mai cewa, an yi wa sansanonin ‘an bindiga da ‘yan Boko Haram ruwan wuta tare da kama wasu daga cikin su.

Sai dai rundunar ba ta bayyana yawan jami’anta da aka kashe ba a yaƙin da su ke yi da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas da sauran sassan Nijeriya da ke fama da matsalar tsaro ba.

RAHOTO: KADUNA

GARGAJIYA: AN BUKACI KABILUN NIJERIYA SU RIKI AL’ADUN SU DA GASKIYA

An yi kira ga daukacin kabilun Nijeriya, su riki al’adun su na gargajiya da daraja, su kuma raya su ta yadda zai zama abin koyi ga na baya.

Kiran ya fito ne, daga bakin daya daga cikin shugabanin Kabilar Nupe Alhaji Ahmad Bidda, a wajen bikin raya al’adu da ya gudana a Kaduna.