Home Labaru Siyasar Imo: Gwamna Emeka Ihedioha Ya Fara Binciken Rochas Okorocha

Siyasar Imo: Gwamna Emeka Ihedioha Ya Fara Binciken Rochas Okorocha

322
0

Sabon gwamnan jahar Imo Emeka Ihedioha, ya kafa kwamitin mutane 8 domin kaddamar da bincike a kan yadda Rochas Okorocha ya kashe kudaden jihar a zamanin mulkin sa daga shekara ta 2011 zuwa 2019.

Gwamnan, ya nada Dakta Abraham Nwanmkwo a matsayin shugaban kwamitin, wanda zai bi diddigin yadda tsohon gwamnan ya kashe kudaden da su ka shiga asusun jihar na tsawon wa’adin mulkin shi.

Mai Magana da yawun gwamnan Chibuike Onyeukwu, ya ce babban aikin da ake bukatar kwamitin ya gudanar shi ne, tabbatar da duk bankunan da kudaden gwamnatin jihar su ke, da sani yawan su da kuma rubuta rahoto a kan hakan.

Haka kuma, ya ce kwamitin zai bi diddigin inda aka samo kudaden da gwamnatin ta kashe wajen gudanar da duk ayyukan da ta gudanar, da bin diddigin adadin kudin ruwan da ya karu a kan kudaden gwamnati da ke bankuna, da kuma bashin da ake bin jihar.

Leave a Reply