Home Labaru Rikicin APC: Adebayo Shitu Ya Goyi Bayan A Tsige Adams Oshiomole

Rikicin APC: Adebayo Shitu Ya Goyi Bayan A Tsige Adams Oshiomole

337
0

Ministan Sadarwa Adebayo Shittu, ya bi sahun jiga-jigan jam’iyyar APC masu goyon bayan a tsige Shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole daga mukamin sa.

Ya ce tantagaryar rashin adalcin da Adams Oshiomhole ya shimfida a cikin jam’iyyar, shi ya janyo aka rasa jihar Oyo da ma sauran jihohin da APC ta sha kaye a zaben gwamnonin da ya gabata.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, Shittu ya ce idan jam’iyyar APC na so ta tsira da sauran mutuncin da ya rage mata, to ta sauke Oshimhole daga shugabancin jam’iyyar APC kawai.

Ministan ya ce, sauke Oshimhole ya zama wajibi idan har jam’iyyar APC na so ta sake cin zabe a shekara ta 2023.

Da ya ke magana a kan hana shi takarar gwamna da aka yi a zaben fidda-gwanin APC, Shittu ya nuna cewa kamar alhakin sa ne ya sa APC ta fadi zaben gwamnan Jihar Oyo.

Leave a Reply