Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta sanar da kama wani gagararren mai laifi da ake zargi da hannu a kisan tsohon shugaban sha’anin mulki a helkwatar rundunar Sojin kasa Manjo Janar Idris Alkali.
Lauyan mai kara Joe-Kyari Gadzama ya bayyana wa kotun cewa, an dauki tsawon lokaci ana neman mutumin bayan ya tsere.
Gadzama, ya nemi kotun ta ba shi dama ya sa sunan mutumin da ake zargi a jerin wadanda ake tuhuma, tare da gudanar da gyare-gyare a tuhume-tuhumen da ake yi masu.
A
watan Nuwamba na shekara ta 2019 ne, ‘yan sanda su ka sanar da cewa akwai
mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Janar Alkali da su ka tsere, wadanda su
ka hada da wani Chuwang Samuel inkiya da Nyam Samuel inkiya.