Home Labarai Siyasa: PDP Ta Soki Kama Danta A Jihar Sokoto

Siyasa: PDP Ta Soki Kama Danta A Jihar Sokoto

102
0
ekFktkpTURBXy82Mjg4MTIxNGNhZTUzMjc5YjUyMjE4MzU0ZTRkMzYwMC5qcGeSlQMAAc0BKMynkwXNAVnMrA
ekFktkpTURBXy82Mjg4MTIxNGNhZTUzMjc5YjUyMjE4MzU0ZTRkMzYwMC5qcGeSlQMAAc0BKMynkwXNAVnMrA

Jam’iyyar PDP reshen jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamun da aka yi wa Shafi’u Umar Tureta, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga tsohon gwamnanr jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta, Hassan Sahabi Sanyinnawal, jam’iyyar ta  ce jami’an ‘yan sanda sun tsare Tureta bisa umarnin gwamnan jihar, Ahmed Aliyu.

A cewar jam’iyyar PDP, an kama Tureta ne saboda yaɗa faifan bidiyo da ke sukar Gwamnan.

Bidiyon da ake magana a kai ya haɗa da wani faifan bidiyo da ke nuna gwamna Aliyu na kokawar yin magana da turanci da kuma wani faifan bidiyo da aka yaɗa na tsabar kudi da ake liƙawa a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar uwargidan Gwamnan.

Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa akwai yiyuwar wasu mutane ne da ke da alaka da ofishin Gwamna ko kuma iyalansa ne suka dauki bidiyon sannan daga baya suka fallasa ga jama’a.

PDP ta kuma ce raba wallafa waɗannan fayafayan bidiyo ba laifi ba ne a ƙarkashin dokar Najeriya, musamman ganin yadda suke nuna abubuwan da nuna taron jama’a da suka shafi Gwamnan da iyalansa.

Leave a Reply