Kotu ta tura hadimin Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, Shafi’u Umar Tureta zuwa gidan gyaran hali bisa zargin ɓatanci ga gwamna mai ci, Ahmad Aliyu, da matarsa, Fatima, a kafafen sada zumunta.
Ana zargin Tureta da yada bayanan karya cewa Gwamna Aliyu ya fadi jarrabawar Turanci a makarantar sakandare da kuma wallafa bidiyon da yake liƙi da daloli a bikin ranar haihuwar Fatima.
An gurfanar da Tureta a kotun majistare a Sakkwato, bayan jami’an tsaro suka kama shi a gidansa.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International Nigeria, ta yi Allah-wadai da kama Tureta,
sannan ta yi kira a sake shi ba tare da wani sharadi ba, tare da sukar gwamantin Jihar Sakkwato bisa take hakkin dan adam.
Sun bayyana cewa tuhume-tuhumen ba su da tushe, kuma sun bukaci gwamnati ta mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi talauci da rashin tsaro a jihar.














































