Home Labarai Siyasa: APC Na Son A Hana Ƙananan Hukumomin Kano Kuɗin Wata-Wata

Siyasa: APC Na Son A Hana Ƙananan Hukumomin Kano Kuɗin Wata-Wata

217
0
courtss 688508 772421 850x460
courtss 688508 772421 850x460

A jihar Kano dai ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin APC da NNPP inda kowannen su ke ƙoƙarin ganin ya shiga gaba a harkokin siyasar jihar mai yawan al’umma a arewacin Najeriya.

Dambarwar baya-bayan nan dai ta faru ne bayan da jam’iyyar APC a jihar ta Kano ta nemi kotu ta dakatar da hukumomin gwamnatin tarayya daga ba ƙananan hukumomin jihar kason kuɗin su na wata-wata.

Wannan kuma zuwa ne bayan da wata kotu ta bayar da umarnin hana duk wata hukuma ko wani yunƙurin dakatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar.

Tun kafin zaɓen ƙananan hukumomin jihar dai ake ta kai ruwa rana tsakanin APC da NNPP wanda har kotu ta bayar da umarnin ka da a gudanar da zaɓen amma daga bisani wata babbar kotun jiha ta bada umarnin a yi zaɓen.

Leave a Reply