Home Labaru Shugabannin ’Yan Bindiga Sun Roki A Tausaya Musu

Shugabannin ’Yan Bindiga Sun Roki A Tausaya Musu

96
0

Wasu kasurguman ‘yan bindiga a yankin Arewa maso
Yammacin Nijeriya musamman jihohin Katsina da Zamfara,
sun yi kira ga gwamnati ta yi musu afuwa.

Wata majiya ta ce, hakan ya na zuwa ne, saboda ci-gaba da kai hare-haren Bom da sojojin Nijeriya ke yi a maboyar ‘yan ta’adda.

A baya dai an ruwaito yadda sojoji suka hallaka ‘yan ta’adda da iyalan su da kuma tarin dabbobin da ake kyautata zaton nasata ne.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigan da aka ce sun yi nadamar shiga ta’addancin da su ka yi, sun kuma tura tawaga zuwa wani taro da aka gudanar a kauyen Gusami da ke karamar hukumar Birnin Magaji a Zamfara su ka bayyana bukatar su.

Wata majiyar leken asiri ta ce, wasu daga cikin manyan tsagerun da wakilan su sun hada da Usman Ruga Kachallah da Alaji Shingi da Lauwali Dumbuluda Shehu Bagiwaye da Shehu Karmuwal da Jarmi Danda.

Leave a Reply